Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Zamfara ta ce mutum 367 sun kamu da cutar mashaƙo, yayin da fiye da 320 daga cikinsu suka warke bayan samun kulawar lafiya.

Daraktan kula da lafiyar al’umma na ma’aikatar, Dakta Yusuf Haske, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Gusau yayin da yake bayani kan halin da ake ciki game da cutar a jihar.

Ya ce kawo yanzu cutar ta yi sanadin mutuwar mutum 44 .

Dakta Haske ya bayyana cewa an ɗauki samfurori daga mutanen da ake zargin sun kamu da cutar, sannan aka gwada su a ɗakunan gwaje-gwaje.

Ya ce daga bisani an sake duba samfurorin a wata cibiya da ke Abuja, inda aka tabbatar da cewa cutar mashaƙo ce.

A cewarsa, bayan tabbatar da barkewar cutar, Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Zamfara, bisa umarnin Gwamna Dauda Lawal, ta ayyana cewa cutar ta ɓarke a jihar.

Ma’aikatar ta ce tana ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin dakile yaɗuwar cutar da kuma kula da waɗanda suka kamu.