Maryam Danazimi Ibrahim, wata ƴar takara daga Najeriya, ta lashe kyautar Riyal 300,000 na Saudiyya , wadda ta kai kusan Naira miliyan 120 , bayan da ta zo ta farko a rukunin mata na haddar Alƙur’ani juz’i 60 tare da Tafsiri , a gasar King Abdulaziz International Qur’an Competition ta duniya karo na 46.

Maryam, wadda ta fito daga Jihar Gombe da ke Arewacin Najeriya, ta yi nasara a rukuni na biyu na gasar, wanda ya ƙunshi haddar Alƙur’ani gaba ɗaya, karatu mai kyau, bin ƙa’idojin Tajweed , da kuma Tafsiri.

Maryam na daga cikin ƴan takara 50 , maza 25 da mata 25, waɗanda aka bayyana a matsayin waɗanda suka yi nasara a rukuni biyar na gasar.

Waɗanda suka yi nasara a rukuni na biyu:

  1. Maryam Danazimi Ibrahim — Najeriya — SAR 300,000
  2. Amat Al-Rahman Badi Mutahhar Kulaib — Bahrain — SAR 275,000
  3. Amani bint Shaya bin Awad Al-Husaiki Al-Harthi — Saudiyya — SAR 250,000
  4. Zainab bint Ibrahim bin Abdulsalam Idris — Saudiyya — SAR 235,000
  5. Shumoukh bint Faiz bin Hamdan Al-Zanbaqi — Saudiyya — SAR 220,000

Ƙasar Saudiyya ta karrama waɗanda suka yi nasara a King Abdulaziz International Qur’an Competition karo na 46, wadda aka gudanar domin haddar Alƙur’ani Mai Tsarki, karatunsa da Tafsirinsa.

Jimillar kuɗaɗen kyaututtukan gasar ta kai Riyal miliyan 10.26 .