Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta ce ta kama mutane 262 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, tare da ceto mutane 27 da aka yi garkuwa da su a ayyukan da ta gudanar a faɗin ƙasar tsakanin ranar 5 zuwa 11 ga Satumba, 2026 .

Rundunar ta kuma ce ta kwato bindigogi 34, harsasai 375 da motoci 11 , yayin da aka kashe wasu mutane 11 da ake zargin ’yan bindiga ne a yayin samamen.

CSP Aniete Iniedu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa kan nasarorin da rundunar ta samu a ƙarƙashin jagorancin Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu .

A cewar sanarwar, waɗanda aka kama na fuskantar zarge-zarge da suka haɗa da garkuwa da mutane, fashi da makami, kisan kai, ’yan bindiga, ƙungiyoyin asiri, safarar mutane, safarar miyagun ƙwayoyi da lalata kayayyakin gwamnati .

Rundunar ta ce a cikin wannan lokaci ta samu rahotannin kisan kai 50, fashi da makami 28, garkuwa da mutane 27 da hare-haren ’yan bindiga 22 .

Nasarorin da aka samu a jihohi

A Jihar Delta , jami’an ’yan sanda sun ceto wani mutum mai shekaru 60 da aka yi garkuwa da shi, bayan musayar wuta da waɗanda ake zargin masu garkuwar ne.

A Jihar Sokoto , an kashe mutane huɗu da ake zargin ’yan bindiga ne yayin wani samame da aka kai domin dakile wani shirin kai hari. Jami’an tsaro sun kuma kwato bindigar AK-47 guda ɗaya da harsasai 28.

A Jihar Kaduna , jami’an tsaro tare da ’yan sa-kai da mafarauta sun kai samame kan sansanonin ’yan bindiga, inda suka ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su tare da kashe mutane biyu da ake zargin ’yan bindiga ne.

Sai dai rundunar ta ce mafarauta uku sun rasa rayukansu , yayin da wani kuma ya samu raunin harbin bindiga a yayin aikin.

A Jihar Akwa Ibom , jami’an tsaro sun dakile wani shirin garkuwa da mutane, tare da kwato bindiga, harsasai da kwale-kwale biyu .

Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike, tare da ƙoƙarin cafke sauran waɗanda ake zargi da hannu a laifukan.