A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar a daren Litinin, 26 ga Oktoba, 2026, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 7:30 na dare a ƙofar gidan malamin da ke Ƙaramar Hukumar Dutsin-Ma.

Sanarwar ta bayyana cewa wasu mutane biyu ɗauke da makamai, waɗanda ke kan babur, sun buɗe wa malamin da abokinsa wuta, inda suka ji musu raunuka masu tsanani.

Bayan samun rahoton harin, jami’in ’yan sanda mai kula da sashen Dutsin-Ma ya jagoranci tawagar jami’ai zuwa wurin. Daga nan aka garzaya da waɗanda abin ya shafa zuwa asibiti mafi kusa domin samun agajin gaggawa.

Sai dai likitoci sun tabbatar da rasuwarsu bayan gudanar da bincike, kamar yadda kakakin rundunar ya bayyana.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, ya bayar da umarnin tura jami’an rundunonin musamman da na gudanar da ayyuka zuwa yankin domin taimaka wa bincike da kuma kamo waɗanda ake zargi da aikata kisan.

Rundunar ta ce an fara bincike kan lamarin, yayin da jami’ai ke ƙara ƙaimi wajen gano waɗanda ake zargin, waɗanda suka tsere bayan harin.

Kwamishinan ’yan sandan ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan mamatan, abokansu da mabiyansu, da kuma al’ummar Ƙaramar Hukumar Dutsin-Ma bisa wannan babban rashi.

Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙarin kamo waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar za ta sanar da jama’a duk wani sabon ci gaba da aka samu game da binciken.

Sheikh Yahya Masussuka ya shahara wajen bayyana ra’ayoyinsa kan wasu batutuwan addini, ciki har da sukar fahimtar wasu malaman Musulunci da kuma kira ga bin Alƙur’ani shi kaɗai. Ya kuma kasance yana sukar wasu hadisai da yake ganin bai kamata a danganta su ga Manzon Allah (SAW) ba.