Kwamishinan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki na jihar, Dr. Bashir Muhammad Achida, ne ya bayyana hakan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta jihar.
Achida ya ce kammala aikin zai taimaka wajen inganta harkokin tattalin arziki a waɗannan ƙananan hukumomi guda huɗu.
Ya ƙara da cewa aikin zai taimaka wajen farfaɗo da harkokin tattalin arziki da zamantakewa, tare da inganta rayuwar al'ummar yankunan.
