Dakarun Sojin Najeriya da ke aikin yaƙi da ’yan bindiga a ƙarƙashin rundunar Operation Fansan Yamma sun sanar da lalata wasu bama-bamai guda uku da aka dasa a Jihar Zamfara.
Kakakin rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Juma’a.
Ya ce haɗin gwiwar jami’an tsaro ya yi nasarar gano tare da kwance bama-baman da aka dasa a babbar hanyar Magami zuwa Dansadau da ke jihar.
A cewarsa, an gudanar da aikin ne tare da taimakon sashen kwance bama-bamai na rundunar ’yan sandan Najeriya, kuma an kammala aikin ba tare da an samu asarar rai ko jikkata kowa ba.
A wani labarin daban, dakarun Operation Fansan Yamma sun kuma dakile wani harin da ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne suka shirya kai wa sansanin soji da ke Maiyama a Jihar Kebbi.
Bayanai sun nuna cewa fiye da mutum 100 dauke da makamai a kan babura ne suka nufi sansanin sojin, amma dakarun suka gano motsinsu tare da fatattakar su.
Kanar Aliyu Danja ya ce maharan sun yi watsi da makamansu tare da tserewa, amma sojojin suka bi sawunsu har suka gano wata maboyarsu.
Ya ce a yayin samamen, sojojin sun ƙwace babura 17 da makamai masu yawa, ciki har da bindigogin AK-47, bindiga mai sarrafa kanta kirar PKT da kuma na’urorin sadarwa.
Rundunar ta ce dakarunta na ci gaba da gudanar da sintiri da sauran ayyukan tsaro domin dakile barazanar ’yan ta’adda da kuma tabbatar da tsaron al’umma a yankin arewa maso yammacin Najeriya.
