Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labaran Soja, Kyaftin Mohammed Goni, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa. Ya ce an kai hare-haren ne tsakanin ƙarfe 1:00 zuwa 2:00 na dare a ranar 26 ga Oktoba, 2026, ta hanyar amfani da ƙarfin sojin sama da na ƙasa.
A cewar rundunar, an gudanar da farmakin ne bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa wasu manyan jagorori da mayaƙan ƙungiyar na cikin wuraren da aka kai wa harin.
Rundunar ta bayyana cewa wannan farmaki wani ɓangare ne na ci gaba da matsin lamba kan ƙungiyoyin ’yan ta’adda da ke aiki a yankin Tafkin Chadi, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
OPHK ta jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukan yaƙi da ta’addanci domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Arewa maso Gabashin Najeriya. Ta kuma ce za ta ci gaba da amfani da sahihan bayanan sirri wajen gano wuraren da ake zargin ’yan ta’adda suna ɓuya.
A ƙarshe, rundunar ta yi kira ga jama’a da su riƙa kai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai cikin lokaci domin taimakawa wajen gudanar da ayyukan yaƙi da ta’addanci.
