Jami'an tsaron Najeriya sun kashe 'yan bindiga uku tare da ceto mutum tara da aka yi garkuwa da su a wani samame da aka gudanar a Jihar Kwara .

An gudanar da aikin ne ta haɗin gwiwar dakarun Rundunar Sojin Najeriya , jami'an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) , dakarun tsaron gandun daji, mafarauta da kuma 'yan sa-kai a yankunan Obbo-Aiyegunle, Ejiu-Ora da Osi da ke Ƙaramar Hukumar Ekiti ta jihar Kwara, kusa da iyakar Jihar Neja.

Rahotanni sun nuna cewa an yi garkuwa da mutanen ne daga al'ummar Eju , kuma masu garkuwar na kan hanyarsu ta bi ta cikin daji zuwa Jihar Neja lokacin da jami'an tsaro suka kai samamen ceto.

A yayin artabun, jami'an tsaron sun kashe mutum uku da ake zargin 'yan bindiga ne, tare da kubutar da dukkan mutanen tara da aka sace.

A cikin 'yan watannin nan, Jihar Kwara na fuskantar ƙaruwar hare-haren 'yan bindiga da sauran masu aikata laifuka kan fararen hula da jami'an tsaro.

A wani mataki na ƙarfafa tsaro, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sabon bataliyar sojoji a jihar a ranar 22 ga Yuli , domin ƙarfafa yaƙi da 'yan bindiga da sauran ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya, ciki har da ƙungiyar Mahmuda , wadda gwamnatin tarayya ta bayyana a matsayin wani reshe na Boko Haram.