Shugaban Siriya, Ahmed al-Sharaa , ya naɗa tsohon shugaban ƙungiyar SDF/YPG, Mazloum Abdi , a matsayin mai ba shi shawara, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar, SANA, ya ruwaito.
Rahoton ya ce Al-Sharaa ya fitar da wata sanarwar doka ranar Alhamis, inda ya naɗa Abdi a matsayin “mai ba da shawara ga Shugabancin Jamhuriyar.”
Matakin na zuwa ne bayan wata yarjejeniya da gwamnatin Siriya da ƙungiyar YPG suka cimma a ranar 29 ga Janairu , wadda ta tanadi tsagaita wuta da kuma shigar da mayakan ƙungiyar cikin hukumomin gwamnatin ƙasar.
A wani taron manema labarai da aka gudanar ranar Talata, Abdi ya bayyana cewa an kawo ƙarshen tsarin ƙungiyar SDF/YPG, tare da fara aiwatar da matakan haɗa sassan da ke ƙarƙashinta cikin hukumomin ƙasar.
An shirya haɗa yankunan da ke ƙarƙashin SDF da gwamnatin Siriya
Yarjejeniyar ta tanadi cewa cibiyoyin farar hula da na soja da ke ƙarƙashin ikon ƙungiyar a arewa maso gabashin Siriya za su koma ƙarƙashin gwamnatin ƙasar.
Hakan ya haɗa da wasu wuraren da ke da muhimmanci ga tattalin arziki da tsaro, ciki har da iyakar ƙasa, filayen jiragen sama da wuraren hako mai da iskar gas .
A baya, SDF, wadda Amurka ke marawa baya, ta kasance tana da iko a wasu sassan arewa maso gabashin Siriya. YPG kuma ta kasance wani muhimmin ɓangare na ƙungiyar.
Gwamnatin Siriya ta sha zargin ƙungiyar da jinkirta aiwatar da yarjejeniyar haɗewa da tsarin gwamnati, musamman bangaren soji.
Matsayar Turkiyya
Turkiyya ta dade tana kira ga ƙungiyoyin da take dangantawa da PKK, ciki har da YPG/SDF, da su ajiye makamansu tare da kawo ƙarshen tsarin ƙungiyoyin.
Ankara ta ce zaman lafiyar Siriya na buƙatar samun gwamnati guda ɗaya da rundunar soji guda ɗaya mai cikakken iko a faɗin ƙasar.
Matakin na baya-bayan nan ya kuma zo ne bayan sanarwar PKK ta kawo ƙarshen tsarin ƙungiyar da kuma dakatar da gwagwarmayarta ta shekaru da dama.
