Attajirin ɗan kasuwar Nijeriya, Aliko Dangote , ya ce samun ɗa namiji da zai ci gaba da riƙe sunan iyalinsa da gadon abin da ya bari ba shi ne babban burinsa ba.
Dangote, mai shekaru 69, ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na ARISE News , yayin da aka tambaye shi ko har yanzu yana fatan samun ɗa namiji.
Ya ce samun ɗa namiji ba lallai ne ya zama tabbacin ci gaba da sunan iyali ko gadon dukiyar da mutum ya bari ba.
Dangote ya ce:
“Wannan, a ganina, ba shi ne babban burina ba. Bari in faɗa kai-tsaye. Ba shi ne babban burina ba, domin a yau kamar yadda muke magana, Allah ne ke sarrafa komai.”
Attajirin ya ƙara da cewa ko da yake mutane na iya yin addu’ar samun ɗa namiji, ba a tabbatar da cewa ɗan zai zama wanda zai ci gaba da kyautata sunan iyali ba.
A cewarsa, wani lokaci ɗa namiji na iya zama sanadin lalacewar sunan zuriya ko jefa iyali cikin matsala.
“Wani lokaci kana iya roƙon Allah Ya ba ka ɗa namiji, amma wannan ɗan shi ne zai iya ɓata sunan zuri’ar da jefa ta cikin matsala. Don haka, wani lokaci idan Allah bai ba ka wani abu ba, kada ka matsa.”
’Ya’yansa mata uku sun isa
Dangote, wanda yake da ’ya’ya mata uku , ya ce bai yi imanin cewa samun ɗa namiji zai sa ya samu abin da ya fi abin da ’ya’yansa mata suka cimma ba.
Ya ce:
“Ban yi imanin cewa da na samu ɗa namiji da zai yi abin da ya fi abin da waɗannan ’ya’ya mata uku nawa suka yi ba.”
Maganganun Dangote na zuwa ne a yayin da a wasu al’ummomin Afirka, musamman a tsakanin al’adun da ke bai wa ɗa namiji muhimmiyar rawa wajen ci gaba da sunan iyali da gadon dukiya.
