Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Injiniya Emmanuel Omuorah, ne ya bayyana hakan yayin wani taron da ƙungiyar ta shirya a ranar Alhamis a jihar Legas.
Omuorah ya ce masu gidajen burodin na fuskantar matsin tattalin arziki sakamakon tsadar makamashi, fulawa, sukari da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen samar da burodi.
Ya bayyana cewa cikin shekaru biyu da suka gabata, mambobin ƙungiyar sun yi asarar makudan kuɗaɗe saboda hauhawar farashin kayayyakin masarufi, inda farashin wasu daga cikinsu ya ninka idan aka kwatanta da na baya.
Shugaban ya kuma koka kan yadda ko basukan da suke karɓa domin gudanar da kasuwancinsu ake caje su da kuɗin ruwa mai yawa, lamarin da ke ƙara jefa su cikin asara maimakon samun riba.
Ya ce a halin yanzu, masu gidajen burodin na fuskantar ƙalubalen ƙara farashin kayayyakinsu saboda matsin tattalin arzikin da al'umma ke ciki, yayin da adadin masu sayen burodi ya ragu sosai.
Haka kuma, ƙungiyar ta bayyana damuwarta kan rashin isa ga mambobinta na tallafin lamunin kuɗi da gwamnati ke bayarwa, duk da irin wahalhalun da suke sha wajen ci gaba da sana'ar.
PBAN ta ce tsadar makamashi na daga cikin manyan dalilan da suka haddasa durƙushewar sana'ar yin burodi a Najeriya, musamman a daidai lokacin da ake fama da hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa.
Ƙungiyar ta yi gargadin cewa idan ba a ɗauki matakan tallafa wa masu sana'ar ba, akwai yiwuwar ƙarin gidajen burodi su daina aiki, lamarin da zai shafi samar da abinci da ayyukan yi a ƙasar.
