Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana a ranar Alhamis cewa babu wata yarjejeniyar tsagaita wuta da ƙungiyoyin ’yan ta’addan Boko Haram da Daesh, tana mai cewa za ta ci gaba da kai hare-hare domin murƙushe ayyukansu.
Sojojin ƙasar sun shafe kusan shekaru 20 suna yaƙi da ’yan ta’adda a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.
Da yake magana yayin wani taron manema labarai kan bayanan sirri da aka gudanar a Abuja, babban birnin ƙasar, mai magana da yawun rundunar, Manjo-Janar Samaila Uba, ya ce nasarorin da dakarun tsaro suka samu a baya-bayan nan, ciki har da kashe ’yan ta’adda, kama waɗanda ake zargi da aikata laifuka da kuma kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su, na nuna cewa ana ci gaba da matsa wa ƙungiyoyin ta’addanci lamba.
Uba ya ce: “Ina son in bayyana ƙarara cewa babu wani abu da ake kira tsagaita wuta. Idan aka yi la’akari da nasarorin da aka samu a wuraren da muke gudanar da ayyuka, a bayyane yake cewa ba ma sassautawa.”
Ya kuma bayyana cewa Nijeriya na tattaunawa da ƙasashen yankin Sahel maƙwabta da suka fice daga Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), domin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da diflomasiyya.
