Kamfanin ya bayyana cewa matakin na daga cikin ƙoƙarinsa na faɗaɗa harkokin kasuwancinsa a nahiyar Afirka, tare da ƙara zuba jari a wajen Najeriya.
Wannan ciniki zai bai wa NGX damar samun gindin zama a Gabashin Afirka, inda kasuwar Nairobi ke taka muhimmiyar rawa wajen hada-hadar kuɗi da zuba jari.
Sai dai kamfanin bai bayyana adadin kuɗin da ya kashe wajen sayen wannan kaso ba.
A shekarar 2024, NGX Group ya kuma zama ɗaya daga cikin masu hannun jari a Kasuwar Hannun Jari ta Habasha.
Ƙoƙarin haɗa kasuwannin hannun jari na Afirka
Kasuwannin hannun jari na ƙasashen Afirka na ƙara ƙoƙarin haɗa kai, domin sauƙaƙa zuba jari tsakanin ƙasashe da bunƙasa tattalin arziƙin nahiyar.
Sai dai wannan yunƙuri na fuskantar wasu ƙalubale da suka shafi gudanarwa da tsarin kasuwanni, musamman wajen sauƙaƙa zirga-zirgar jarin masu zuba jari daga wata ƙasa zuwa wata.
NGX Group ya ce sayen wannan kaso na hannun jari zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin kan tattalin arziƙin yankin, faɗaɗa damar zuba jari da kuma samar da ƙarin ƙima ga masu hannun jari a dogon lokaci.
Shugaban NGX Group, Umaru Kwairanga, ya ce kasuwannin hannun jari na Afirka na cikin wani muhimmin mataki na bunƙasa, inda burin haɗa su ke sauyawa daga fata zuwa dabarun da ake aiwatarwa.
Kenya a matsayin cibiyar hada-hadar kuɗi
Babban Jami’in Gudanarwa na NGX Group, Temi Popoola, ya bayyana Kenya a matsayin ɗaya daga cikin muhimman cibiyoyin hada-hadar kuɗi a Gabashin Afirka.
Ya ce zuba jarin da kamfanin ya yi a Kasuwar Hannun Jari ta Nairobi zai faɗaɗa hanyoyin samun ribar zuba jari ga NGX Group a wajen Najeriya.
Popoola ya ƙara da cewa kasuwannin biyu sun riga sun nuna irin amfanin haɗin kai ga kamfanoni, masu zuba jari da kuma masu hannun jari.
