A yayin wasan, ’yan wasan Najeriya, ciki har da Awawu Bashiru da Oluebube Umejiaku, sun zura ƙwallaye biyu a ragar Japan, kafin ƙungiyar ta samu nasarar rama ƙwallo guda.

Duk da ƙoƙarin da Japan ta yi na dawowa wasan, Flamingos ta samu nasarar riƙe jagorancinta har zuwa ƙarshen fafatawar da aka gudanar a filin wasa na Mohammed VI.

Wannan nasara ta sanya Najeriya zama ƙasa ta farko a nahiyar Afirka da ta lashe Kofin Duniya na Mata na ’yan ƙasa da shekara 17, tare da kawo ƙarshen dogon jiran da nahiyar ke yi na samun wannan nasara.

Nasarar ta kuma zama wani muhimmin tarihi ga ƙwallon ƙafar mata a Najeriya da kuma nahiyar Afirka baki ɗaya.