Aƙalla mutum biyar ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 41 suka ɓace bayan wani jirgin ruwa ɗauke da sama da fasinjoji 250 ya kama da wuta a tekun Indonesia.
Hukumar Ceto ta Ƙasa ta Indonesia ta bayyana cewa jirgin, mai suna KMP Mutiara Sentosa 2 , ya kama da wuta ne yayin da yake tafiya daga birnin Surabaya na lardin Gabashin Java zuwa Makassar a lardin Sulawesi ta Kudu.
Rahotanni sun nuna cewa fasinjoji da dama sun sanya rigunan ceton rai, yayin da wasu suka yi tsalle cikin teku domin gujewa gobarar da ta bazu a mafi yawan sassan jirgin.
Jami'an ceto na ci gaba da aikin neman waɗanda suka ɓace tare da ceto sauran fasinjojin da abin ya shafa.
Har yanzu dai ba a bayyana musabbabin tashin gobarar da ta rutsa da jirgin ba, yayin da bincike ke ci gaba.
