Aƙalla mutane 13 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata a wasu hare-hare daban-daban da aka kai kan al’ummomi a ƙananan hukumomin Jos ta Kudu, Mangu da Riyom na Jihar Filato.
Hare-haren sun faru ne a daren Lahadi, inda mutane tara da ke cikin wata mota mai tafiya zuwa Jos suka mutu bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun buɗe musu wuta a yankin Dungus da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu.
Mai magana da yawun ƙungiyar Berom Youth Moulders (BYM) , Rwang Tengwong, ya ce harin ya faru da misalin ƙarfe 9:40 na dare.
A cewarsa, fasinjojin na kan hanyarsu ta zuwa Jos ne lokacin da maharan suka buɗe wa motarsu wuta.
Ya ce an garzaya da wasu daga cikin waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci domin kula da su, amma daga bisani wasu daga cikinsu suka mutu.
Tengwong ya kuma bayyana cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe mamba ne na Operation Rainbow , yana mai bayyana harin a matsayin abin takaici.
An kashe mutane biyu a Mangu
A wani hari na daban, wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne sun kai hari kan al’ummar Vodni , da ke gundumar Pushit a Ƙaramar Hukumar Mangu.
Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne cikin dare, inda suka kashe mutane biyu tare da jikkata wasu huɗu da harbin bindiga.
Waɗanda suka jikkata na samun kulawa a wani asibiti da ke garin Mangu.
An kuma kai hari a Riyom
Haka kuma, a Ƙaramar Hukumar Riyom, an kashe wasu mutane biyu a wani hari da aka kai a yankin Tahoos , kusan a lokaci guda da sauran hare-haren.
Sabbin hare-haren sun ƙara haifar da fargaba da damuwa kan matsalar tsaro a wasu sassan Jihar Filato, yayin da mazauna yankunan ke ci gaba da kira ga hukumomi da su ƙara matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.
’Yan sanda sun tabbatar da hare-haren
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Filato, Ayo Faniyan , ya tabbatar da faruwar hare-haren, amma ya ce rundunar tana ci gaba da tattara cikakkun bayanai kan abubuwan da suka faru.
Kwamishinan ya ce rundunar za ta fitar da sanarwar hukuma da zarar ta samu cikakken bayani kan hare-haren.
