Yayin da wasu 'yan kasuwa ke kashe makudan kuɗaɗe wajen sayen man fetur domin gudanar da janareto, wasu masana'antu na fama da tsadar samar da kayayyaki, lamarin da ke iya janyo hauhawar farashinsu a kasuwa.

A gidaje kuma, rashin ingantacciyar wutar lantarki na ƙara tsananta wa jama'a wahalhalun rayuwa tare da kawo cikas ga harkokinsu na yau da kullum.

Haka kuma, a asibitoci, makarantu da sauran muhimman cibiyoyi, samun wutar lantarki mai ɗorewa na da matuƙar muhimmanci wajen gudanar da ayyuka yadda ya kamata. Musamman a asibitoci, wutar lantarki na taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da na'urorin kula da marasa lafiya da kuma ceton rayuka.

Duk gwamnatocin da suka jagoranci Najeriya a baya sun sha yin alkawarin magance matsalar wutar lantarki, amma har yanzu matsalar na ci gaba da kasancewa babbar ƙalubale. Wasu ma na ganin cewa, maimakon samun sauƙi, matsalar na ƙara taɓarɓarewa, lamarin da ke janyo damuwa ga jama'a da masu gudanar da harkokin kasuwanci.