Matatar man fetur ta Dangote ta samu gagarumar buƙata daga masu zuba jari, inda aka yi rajistar neman sayen hannayen jarin da darajarsu ta haura Naira biliyan 10 cikin mintuna kaɗan bayan fara sayar da hannayen jarin ga jama’a a ranar Litinin.
Jami’an kasuwar hannayen jari ta Nijeriya sun ce dubban masu zuba jari ne suka nuna sha’awar sayen hannayen jarin, yayin da ake sa ran cinikin zai kasance ɗaya daga cikin manyan IPO da aka taɓa gudanarwa a Afirka.
Shugaban Access Holdings, Aigboje Aig-Imoukhuede , ya ce an samu buƙatun sayen hannayen jari na biliyoyin naira daga dubban masu zuba jari cikin ɗan lokaci bayan buɗe cinikin.
Ya bayyana hakan ne yayin bikin ƙaddamar da sayar da hannayen jarin a Nigerian Exchange (NGX) da ke Legas.
Shugaban NGX, Umaru Kwairanga , shi ma ya tabbatar da cewa an riga an samu buƙatun sayen hannayen jarin da darajarsu ta haura Naira biliyan 10 , tun bayan buɗe cinikin da misalin ƙarfe 8 na safe.
Ana son tara dala biliyan 1.6
Sayar da hannayen jarin, wanda aka fi sani da Initial Public Offering (IPO) , zai gudana daga 14 ga Satumba zuwa 13 ga Oktoba .
Matatar na da burin tara kusan dala biliyan 1.6 daga masu zuba jari a faɗin Afirka, tare da samun har zuwa masu hannayen jari miliyan 10 .
Ana sa ran za a fara cinikin hannayen jarin Matatar Dangote a kasuwar hannayen jari ta Nijeriya a watan Nuwamba .
Za a faɗaɗa ƙarfin tace man
A cewar kamfanin, za a yi amfani da kuɗin da aka tara wajen faɗaɗa ƙarfin tace man matatar daga ganga 700,000 a kowace rana zuwa ganga miliyan 1.4 a kowace rana nan da shekarar 2030.
Matatar da ke kusa da Legas mallakin hamshakin ɗan kasuwa, Aliko Dangote , ce. Ta fara aiki a shekarar 2024.
Idan ta kai cikakken ƙarfin aikinta, ana sa ran matatar za ta kasance ɗaya daga cikin manyan matatun mai masu tsarin tacewa guda ɗaya a duniya, tare da taimakawa wajen ƙara ƙarfin Nijeriya na tace ɗanyen man da take samarwa a cikin gida.
Darajar matatar ta kai dala biliyan 49
An kiyasta darajar Matatar Dangote a kusan dala biliyan 49 a cikin shirin IPO ɗin.
Masu nazari sun ce fara cinikin hannayen jarin matatar a kasuwar hannayen jari na iya ƙara jimillar darajar kamfanonin da ake cinikinsu a kasuwar hannayen jari ta Nijeriya da kusan kashi ɗaya bisa uku .
Aliko Dangote ne ya buɗe bikin sayar da hannayen jarin da misalin ƙarfe 9:35 na safe a Legas, tare da manyan jami’an matatar da wakilan wasu cibiyoyin hada-hadar kuɗi daga sassan Afirka.
