Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa matar wani babban jami'in kula da harkokin kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP , tare da ɗanta mai shekara 11, sun miƙa wuya ga dakarun Operation Hadin Kai a ƙauyen Kusuma da ke Jihar Borno.
A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce binciken farko ya nuna cewa mijin matar, wanda ake bayyana a matsayin babban kwamandan ISWAP, ya miƙa wuya ga sojoji a ranar 25 ga Yuli , kuma shi ne ya umarce ta da ta fito daga maɓoyarsu tare da ɗansu domin su miƙa wuya.
Haka kuma, rundunar ta ce dakarunta sun kai wani samame na daban a yankin Turoh bayan samun sahihan bayanan sirri kan motsin mayaƙan ƙungiyar.
A cewar sanarwar, mayaƙan sun tsere kafin isowar sojojin, inda suka bar wasu kayayyaki a wurin.
Bayan binciken yankin, dakarun sun ƙwato babura biyu da kuma tarin miyagun ƙwayoyi , waɗanda ake zargin mayaƙan sun bari yayin da suke tserewa.
Rundunar ta jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da hare-hare da suka dogara da sahihan bayanan sirri domin daƙile ayyukan ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
