Mataimakin Shugaban Ƙasar Turkiyya, Cevdet Yilmaz, ya buƙaci ƙasashen Musulmi su haɗa kai wajen adawa da abin da ya kira ta’asar Isra’ila tare da ƙara tallafa wa al’ummar Falasɗinu.
Yilmaz ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin jagorantar zaman rufe taron Kwamitin Haɗin Kan Tattalin Arziki da Kasuwanci na Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmi (OIC), wato COMCEC karo na 42, a birnin Istanbul na Turkiyya.
Ya ce duk da sanarwar tsagaita wuta, gwamnatin Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, na ci gaba da kai hare-hare kan Falasɗinawa, tare da hana kai agajin jinƙai da kuma ƙin aiwatar da mataki na gaba na yarjejeniyar tsagaita wutar.
A cewarsa, waɗannan matakai na ƙara tsananta wahalhalun da al’ummar Falasɗinu ke fuskanta a kullum.
Yilmaz ya jaddada cewa wajibi ne ƙasashen Musulmi su tsaya tsayin daka wajen kare Falasɗinawa, musamman mazauna Gaza, ta hanyar amfani da dukkan hanyoyin da suke da su.
Ya kuma bayyana cewa taron COMCEC ya nuna aniyar ƙasashen Musulmi ta magance rikice-rikicen siyasa da na tsaro da ke addabar duniyar Musulunci ta hanyar diflomasiyya.
Dangane da tallafin Falasɗinu, Yilmaz ya bayyana cewa shirin Al-Quds na COMCEC ya ƙaddamar da sabbin ayyuka 10 a wannan shekara, baya ga ayyuka 28 da aka riga aka kammala domin tallafa wa Falasɗinawa.
Haka kuma, ya yi maraba da ci gaban da aka samu ƙarƙashin shirin Syria na COMCEC, wanda ke da nufin ƙarfafa ƙwarewar mutane da cibiyoyi tare da farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar ta hanyar ayyuka biyar.
A ɓangaren tattalin arziki, Yilmaz ya sake jaddada burin OIC na ƙara yawan cinikayya tsakanin ƙasashe mambobinta zuwa kashi 25 cikin 100 na jimillar cinikayyarsu.
Ya ce faɗaɗa tsarin fifita cinikayya tsakanin ƙasashen OIC, ƙarfafa zuba jari da kasuwanci na zamani, da sauƙaƙa harkokin kasuwanci za su taimaka wajen bunƙasa haɗin gwiwa.
Ya ƙara da cewa tattaunawar ministoci ta wannan shekara ta mayar da hankali kan samar da ingantattun hanyoyin samun kuɗaɗen gudanar da kasuwanci, musamman domin tallafa wa ƙananan masana’antu da matsakaitan ’yan kasuwa wajen fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.
Yilmaz ya kuma yi kira da a ƙarfafa cibiyar sasanta rikice-rikicen kasuwanci ta OIC domin warware takaddamar kasuwanci da zuba jari cikin gaggawa da adalci.
Bugu da ƙari, ya buƙaci a gaggauta fara aiwatar da shirin Shaidar Halal na Musulunci, domin sauƙaƙa amincewa da takardun shaidar halal tsakanin ƙasashe mambobin ƙungiyar da kuma kawar da shingayen kasuwanci.
Ya bayyana cewa a ƙarƙashin tsarin tallafa wa ayyukan COMCEC, ana gudanar da ayyuka 31 a wannan shekara a fannoni daban-daban, ciki har da ilimi, haɗin gwiwar fasaha, ƙwarewar zamani da bunƙasa cibiyoyi.
A cewarsa, tun daga shekarar 2013, shirin ya tallafa wa ayyuka 209, inda dukkan ƙasashe mambobin OIC suka samu damar shiga.
Ya kuma bayyana cewa ƙasashe 24 da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa 12 sun gudanar da tattaunawa kusan 62 a gefen taron.
A ƙarshe, Yilmaz ya sanar da cewa taron ministocin na shekara mai zuwa zai mayar da hankali kan amfani da hanyoyin kuɗaɗen Musulunci wajen tabbatar da wadatar abinci, yana mai bayyana hakan a matsayin muhimmin batu ga ci gaban ƙasashe mambobin OIC.
