Masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafar Najeriya sun gabatar da shawarwari daban-daban kan yadda za a kawo gyara a tsarin gudanar da ƙwallon ƙafar ƙasar.

Tattaunawar na zuwa ne bayan Najeriya ta gaza samun damar shiga gasar Kofin Duniya sau biyu a jere, yayin da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) ke neman shawarwarin masu ruwa da tsaki kan makomar harkar ƙwallon ƙafar ƙasar.

Shugabannin hukumomin ƙwallon ƙafa na jihohi (FA) sun yi kira da a aiwatar da sauye-sauye ta hanyar tsarin cikin gida na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF).

A gefe guda kuma, wakilan ’yan wasa, koci-koci da alkalai sun bukaci a faɗaɗa shigar masu ruwa da tsaki cikin tsarin tattaunawar da kuma yanke shawarar da za a ɗauka.

An fara tattaunawar ne ranar Litinin, bayan ajiye tsohon shugaban NFF, Ibrahim Gusau. Ana sa ran za a ci gaba da tattaunawar ranar Talata.

FIFA da CAF za su nazarci shawarwarin da ƙungiyoyi daban-daban suka gabatar kafin su ba da shawara kan matakin da ya dace a ɗauka domin kawo gyara.

Hukumomin jihohi sun bayyana matsayinsu

Yakubu Sarma, shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Jihar Gombe kuma shugaban tawagar shugabannin hukumomin ƙwallon ƙafa na jihohi, ya ce suna goyon bayan gyare-gyare, amma suna ganin ya kamata a aiwatar da su ta hanyar tsarin da dokokin NFF suka tanada.

Ya ce harkar ƙwallon ƙafar Najeriya ba ta cikin wani rikici da zai sa a rushe tsarin da ake da shi, yana mai nuni da cewa gasar lig-lig na gudana, ƙungiyoyin Najeriya na fafatawa a wasannin nahiyar, yayin da ƙungiyoyin ƙasa ma ke ci gaba da gudanar da ayyukansu.

“Muhimmin batu da muka gabatar wa FIFA a matsayin mambobin tawagar da ke wakiltar hukumomin ƙwallon ƙafa na jihohi shi ne harkar ƙwallon ƙafar Najeriya ba ta cikin wani rikici, domin gasar lig ɗinmu na tafiya, ƙungiyoyin ƙwallon ƙafarmu na wasa a matakin nahiya, ’yan matanmu na buga wasannin ƙasa da ƙasa, sannan sakatariyar NFF na aiki,” in ji Sarma.

Sarma ya ƙara da cewa hukumomin ƙwallon ƙafa na jihohi ba sa adawa da gyare-gyare, yana mai cewa wasu daga cikin sauye-sauyen da ake magana a kansu an riga an tanade su cikin dokokin NFF.

’Yan wasa da koci-koci na neman ƙarin wakilci

Wakilan ’yan wasa, koci-koci da alkalai sun kuma yi kira da a faɗaɗa yawan masu ruwa da tsaki da za su shiga tattaunawar, domin a samu ra’ayoyi daga ɓangarori daban-daban na harkar.

Ana sa ran FIFA da CAF za su kammala nazarin shawarwarin da aka gabatar kafin su yanke shawara kan matakin gaba na aikin gyaran harkar ƙwallon ƙafar Najeriya.

Tattaunawar na gudana ne a daidai lokacin da Hukumar Wasanni ta Najeriya ke matsa kaimi domin ganin an samar da sauyi a tsarin gudanar da ƙwallon ƙafa, bayan gazawar Super Eagles na samun gurbin shiga gasar Kofin Duniya sau biyu a jere.