An ruwaito cewa matakin ya biyo bayan wani taron sirri da mamallakin ƙungiyar, Sir Jim Ratcliffe, ya gudanar da manyan jami'an gudanarwarta, Omar Berrada da Jason Wilcox, a birnin Monaco.
Tun kwanakin baya ake ta rade-radin yiwuwar sallamar Carrick, yayin da shugabannin ƙungiyar ke nazarin wanda zai maye gurbinsa.
Rahotanni sun nuna cewa Manchester United ta fara nuna shakku kan makomar kocin ne bayan rashin nasarar da ta sha da ci 3-0 a hannun Bournemouth a ranar 25 ga Oktoba.
Haka kuma, canjaras ɗin da ƙungiyar ta yi da Aston Villa da ci 4-4 a ranar Lahadi ya ƙara jefa ta cikin mawuyacin hali.
A halin yanzu, ƙungiyar tana matsayi na 18 a teburin gasar Firimiya, wanda hakan ya kasance ɗaya daga cikin mafi munin fara kakar wasa da ta yi cikin sama da shekaru 40.
Sanarwar Manchester United kan sallamar Carrick
A cikin sanarwar da ta fitar, Manchester United ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne bayan nazarin halin da ƙungiyar ke ciki, inda ta ce tana buƙatar sauyi domin cimma burinta.
Ƙungiyar ta kuma yaba da gudummawar da Michael Carrick ya bayar, tana mai cewa zai ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin gwarazan da suka taka muhimmiyar rawa a tarihinta.
Ta ƙara da cewa ba za a manta da jagorancinsa da nasarorin da ya samu a kakar wasan da ta gabata ba.
