Pochettino ya sanya hannu kan kwantiragin shekara biyu da rabi da ƙungiyar ta Old Trafford, wanda zai sa ya ci gaba da jagorantar ta har zuwa shekarar 2029.

Hakan na zuwa ne bayan Manchester United ta yanke shawarar raba gari da Carrick, wanda ya kasa cimma nasarar da ake fata a lokacin da yake jagorantar ƙungiyar.

BBC ce ta tabbatar da labarin naɗin sabon mai horaswar.