Majalisar dokokin Bangladesh ta zaɓi Mirza Fakhrul Islam Alamgir a matsayin sabon shugaban ƙasar, a wani zaɓen shugaban ƙasa na farko da aka fafata a kai cikin shekaru 35.
Mista Alamgir, wanda ke cikin jam’iyyar mai mulki ta Bangladesh Nationalist Party (BNP) , ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ‘yan adawar tsohuwar Firaminista Sheikh Hasina , wadda aka hambarar da ita a shekarar 2024 bayan zanga-zangar ɗalibai da ta rikide zuwa rikicin siyasa.
Alamgir ya taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar jam’iyyar BNP a cikin shekaru masu cike da ƙalubale, kuma hukumomi sun taɓa kama shi sau da dama.
Zaɓensa ya zo ne a daidai lokacin da Tarique Rahman ke cika watanni shida a matsayin Firaministan Bangladesh.
A tsarin mulkin Bangladesh, shugaban ƙasa ba shi da manyan ikon zartarwa, domin mafi yawan iko yana hannun firaminista. Sai dai a ƙarƙashin sauye-sauyen kundin tsarin mulkin da ake shirin yi, ana iya ƙara wa ofishin shugaban ƙasar wasu ƙarin iko domin samar da daidaito tsakanin manyan shugabannin ƙasar.
