Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke zaɓen fidda gwani da ya samar da Bashir Abdullahi Gaddafi a matsayin ɗan takarar jam’iyyar ADC mai neman kujerar Akko a Majalisar Wakilan Tarayya a zaɓen 2027.
Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Vera E. Ibrahim, ta umarci a gudanar da sabon zaɓen fidda gwani na jam’iyyar a mazabar cikin kwanaki 21.
Haka kuma, kotun ta bayar da umarnin janye takardar shaidar nasarar zaɓen da aka bai wa Gaddafi nan take.
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da Adamu Hassan Kashere ya shigar, inda ya ƙalubalanci yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwani da ya samar da Gaddafi a matsayin ɗan takarar ADC.
Kashere ya yi zargin cewa ba a gudanar da zaɓen fidda gwani yadda ya kamata a sassan mazabu daban-daban na Ƙaramar Hukumar Akko ba.
Mai ƙarar ya kuma ƙalubalanci cancantar Gaddafi, bisa zargin cewa ma’aikacin gwamnati ne da bai bar aikinsa a hukumance ba kafin shiga takarar fidda gwani, kuma yana ci gaba da karɓar albashinsa na wata-wata.
Sai dai kotun ta bayyana cewa Kashere bai gabatar da isassun hujjojin da za su tabbatar da zargin cewa Gaddafi ya ci gaba da karɓar albashinsa a lokacin da yake takarar ba.
Kotun ta kuma amince cewa Gaddafi ɗan jam’iyyar ADC ne kuma yana da cancantar shiga zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.
A yayin shari’ar, Kashere ya nemi gabatar da wasu takardu domin ƙarfafa hujjojinsa, amma aka samu saɓani kan karɓar takardun a matsayin hujjoji a kotu.
Kashere ya shigar da ƙarar ne kan Gaddafi, jam’iyyar ADC da kuma Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), yana ƙalubalantar tsarin da aka bi wajen zaɓen Gaddafi a matsayin ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilan Tarayya.
