Mai ƙarar ya zargi shirin da yaɗa abubuwan da suka saɓa wa koyarwar Musulunci da al’adun Hausawa, yana mai cewa hakan na iya yin illa ga tarbiyyar iyalinsa, musamman matansa da ’ya’yansa.

Ya kuma buƙaci kotun ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan wanda ake ƙara.

Sai dai lauyan wanda ake ƙara, Barista Aliyu Usman Hajji, ya kare shirin, yana mai cewa fina-finai wata hanya ce ta fasaha da ilmantarwa, don haka ya kamata a duba cikakken labarinsu kafin a yanke hukunci a kansu.

Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ne ya jagoranci zaman kotun, inda ya amince da buƙatar lauyan wanda ake ƙara na shigar da rubutaccen martani.

Bayan haka ne kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 18 ga Disamba domin ci gaba da shari’ar.