An yi Allah-wadai a sassa daban-daban na duniya kan matakin Amurka na ƙara kakaba takunkumin kuɗi ga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya, ICC.
Kotun ta ICC da kuma Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya sun bayyana matakin hana mu’amalar kuɗi da kotun a matsayin wani hari kan tsarin tabbatar da adalci a matakin ƙasa da ƙasa.
Kasashen Canada da Japan da wasu ƙasashen Turai sun sake jaddada goyon bayansu ga kotun, wadda ke da alhakin bincike da gurfanar da mutanen da ake zargi da aikata manyan laifuka, ciki har da laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil’adama.
A nasa ɓangaren, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce Shugaba Donald Trump ba zai amince da abin da ya kira kotu marar bin ƙa’ida ta gurfanar da ’yan Amurka a gaban shari’a ba.
Matakin na Washington ya ƙara janyo muhawara kan ikon kotun ta ICC da kuma dangantakar da ke tsakanin Amurka da ƙasashen da ke goyon bayan ayyukanta.
