Kamfanin Microsoft ya fitar da wani sabon kundin ƙa’idojin gudanar da amfani da fasahar AI, wanda aka tsara domin tabbatar da cewa mutane ne ke da iko kan yadda tsarin AI ke aiki.

Kamfanin ya bayyana cewa kundin, wanda ya ginu kan manufar Humanist AI, na da nufin tabbatar da cewa fasahar AI ta kasance ƙarƙashin kulawar ɗan Adam, musamman a lokacin da ake ƙara samun damuwa kan matsalolin tsaro da haɗarin amfani da fasahar ba bisa ka’ida ba.

Microsoft ya ce ya kamata a tsara tsarin AI ta yadda zai mutunta ikon ɗan adam, tare da tabbatar da cewa ana iya sa ido da kuma tantance yadda yake yanke hukunci ko gudanar da ayyukansa.

Matakin na zuwa ne yayin da ake ƙara samun muhawara a Duniya kan yadda za'a daidaita amfani da AI, musamman game da tsaro, sirrin bayanai da kuma yiwuwar fasahar ta yi aiki ba tare da isasshen sa hannun ɗan adam ba.

Kamfanin ya ce manufarsa ita ce a samar da tsarin AI da zai kasance mai amfani ga bil’adama, yayin da aka tabbatar da cewa ɗan adam ne ke da alhakin yanke muhimman shawarwari, ba fasahar AI ita kaɗai ba.