A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na ƙasa, Mohammed Khalil Bello, ya fitar, ya bayyana cewa shirin zai fara ne da makonni biyu na tuntuɓa da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, kafin a shafe wata guda ana aiwatar da matakan samar da zaman lafiya.

KACRAN ta ce akwai ƙwararrun shugabanni da masana harkokin tsaro a Arewa waɗanda za su iya taka muhimmiyar rawa wajen warware matsalolin tsaro da suka addabi yankunan.

Ƙungiyar ta jaddada cewa samar da zaman lafiya a Arewa na da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin Najeriya, kasancewar Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya na daga cikin manyan yankunan da ake samar da abinci a ƙasar.

Ta bayyana cewa rashin tsaro na ci gaba da yin barazana ga noma, kiwo da sauran harkokin tattalin arziki, lamarin da ke shafar rayuwar al'ummomin yankunan.

Haka kuma, KACRAN ta yi nuni da abin da ta bayyana a matsayin nasarar amfani da tattaunawa wajen rage rikice-rikice a jihohin Kaduna da Katsina. Saboda haka, ta yi kira ga sauran gwamnonin yankunan da su rungumi tattaunawa da sulhu a matsayin hanyoyin magance matsalolin tsaro.

Sai dai ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa kafa ƙungiyoyin sa-kai bisa tushen ƙabila na iya ƙara dagula matsalar tsaro maimakon taimakawa wajen magance ta.

A ƙarshe, KACRAN ta buƙaci gwamnati ta amince da shirin zaman lafiyar da ta gabatar, tare da ɗaukar matakan da suka dace kan duk waɗanda suka ƙi bin yarjejeniyoyin sulhu da aka cimma.

Sai dai wannan ƙiyasin na kwanaki 45 na KACRAN ne; ba tabbaci ba ne cewa za a kawo ƙarshen rashin tsaro a cikin wannan lokaci. Nasarar shirin za ta dogara ne da amincewar gwamnati, haɗin kan masu ruwa da tsaki da kuma yadda za a aiwatar da matakan tsaro da sulhu.