Iyayen yaran da aka sace a jihar Borno sun gudanar da zanga-zanga a garin Uba ranar Alhamis, domin neman gwamnatin Najeriya ta gaggauta ceto kusan yara 100 da ake tsare da su a hannun masu garkuwa da mutane a yankin.
A ranar 15 ga watan Mayu , wasu mahara da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka kai hari wata makaranta da ke ƙauyen Mussa, kusa da dajin Sambisa, inda suka sace kimanin ɗalibai 45 , ciki har da ƙananan yara. Har yanzu dai yaran na hannun masu garkuwa da su.
Zanga-zangar ta nuna irin damuwar da iyaye ke ciki game da ci gaba da sace mutane da hare-haren ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP, duk da kasancewar jami’an tsaro a yankin.
Ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP sun shafe sama da shekaru 15 suna kai hare-hare da kuma sace ɗalibai a makarantun yankin.
Baya ga sace ɗaliban ƙauyen Mussa, an kuma kai hari wata makaranta da ke ƙauyen Lassa a ranar 29 ga watan Yuni , inda aka sace ɗalibai 36 da wani malami. Har yanzu su ma suna hannun masu garkuwa da su.
A watan da ya gabata ne hukumomin Najeriya suka samu nasarar kuɓutar da wasu ɗalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a jihar Oyo , da ke kudu maso yammacin ƙasar.
