Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya sanar da cimma matsaya da mahukuntan Nijar kan bayar da sabon rancen kuɗi har dala miliyan 203, domin taimaka wa ƙasar wajen farfaɗo da tattalin arziƙinta da aiwatar da gyare-gyare a wannan fanni cikin shekaru uku masu zuwa.
Sanarwar IMF, wadda shugabar tawagar asusun da ta ziyarci Nijar, Julia Bersch, ta sanya wa hannu, ta ce an cimma yarjejeniyar ne yayin tattaunawar da wakilan asusun suka yi da mahukuntan ƙasar a birnin Yamai, babban birnin Nijar.
A cewar sanarwar, yarjejeniyar ta shafi tsawon watanni 38, amma ana jiran amincewar hukumar gudanarwar IMF kafin a fara sakin kuɗaɗen rancen.
IMF ya bayyana cewa rancen da ya bai wa Nijar a baya ya taimaka wajen rage wasu matsalolin tattalin arziƙin ƙasar. Sai dai asusun ya ce Nijar na ci gaba da fuskantar ƙalubale da dama, lamarin da ya sa ake ganin sabon tallafin kuɗin ya zama dole.
Sanarwar ta nakalto Julia Bersch tana cewa matsalolin tattalin arziƙi daga fannoni daban-daban sun ƙara wa Nijar nauyi, tare da kawo cikas ga ƙoƙarin ƙasar na aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziƙi tsakanin shekarun 2025 zuwa 2029, ƙarƙashin shirin rancen da ta karɓa a baya.
IMF na sa ran cewa, tare da sabon tallafin da kuma bunƙasar wasu muhimman sassa, tattalin arziƙin Nijar zai iya samun ƙaruwar kashi bakwai cikin ɗari a shekarar 2027, musamman sakamakon gudunmawar noma da makamashi.
