An sanar da dakatarwar ne ranar Juma’a, bayan tattaunawa tsakanin shugabannin hukumar kwastam da tawagar hukumar FCC.
Hukumar kwastam ta ce ta dakatar da horaswar a cibiyoyinta biyu domin ba da damar ci gaba da shawarwari da kuma warware matsalolin da suka taso.
Hukumar FCC ta nuna damuwa kan yadda aka ce ba a gayyaci wasu masu neman aikin da aka wallafa sunayensu a cikin jerin waɗanda suka yi nasara ba, yayin da wasu waɗanda ba a wallafa sunayensu ba suka samu gayyata zuwa horaswar.
Hukumar ta kuma ce ta samu ƙorafe-ƙorafe daga sama da masu neman aikin 500, waɗanda suka yi zargin cewa sun kammala dukkan matakan da ake buƙata, ciki har da gwajin lafiya, amma daga baya aka cire su daga cikin waɗanda za a ɗauka aiki.
Hukumar kwastam ta fara aikin ɗaukar ma’aikatan ne a ranar 27 ga Disamban 2024, inda ta sanar da guraben aiki 3,927 a rukuni-rukuni uku. Fiye da mutane 573,000 ne suka nemi aikin, yayin da aka tantance 286,697 domin matakan tantancewa na gaba.
An wallafa jerin sunayen mutane 3,852 da suka yi nasara tsakanin ranakun 28 zuwa 30 ga Yulin 2026. An fara horas da su ranar 9 ga Oktoba, kafin daga bisani aka sanar da dakatarwar.
Hukumar FCC ta bukaci gudanar da bincike kan tsarin ɗaukar ma’aikatan, sannan ta ce ta yanke shawarar dakatar da aikin ɗaukar ma’aikatan har sai an warware matsalolin da suka taso. Ta kuma shigar da ƙara a kotu kan hukumar kwastam saboda ƙin dakatar da horaswar tun da farko.
Sai dai Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, ya sake jaddada aniyar hukumar ta yin aiki tare da FCC domin tabbatar da adalci da gaskiya a tsarin ɗaukar ma’aikata.
