Wani jami'in sojin gwamnatin Yemen ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mayaƙan Houthi masu samun goyon bayan Iran sun kammala ƙwace dukkan yankunan da sojojin gwamnatin Yemen ke iko da su a gabar yammacin Tekun Maliya.
Jami'in ya ce mayaƙan Houthi sun ƙwace tashar jiragen ruwa ta Dhubab , da tsibirin Mayun (Brim) mai muhimmanci ga ayyukan soji, baya ga tsibiran Greater Hanish da Lesser Hanish , waɗanda ke kusa da mashigar Bab al-Mandab.
Rahotanni sun ce dakarun gwamnatin Yemen da ke samun goyon bayan Saudiyya sun janye daga waɗannan yankuna.
A ranar Alhamis ma, mayaƙan Houthi sun sanar da ƙwace tashar jiragen ruwa ta Mocha , matakin da ya ƙara musu tasiri a kan mashigar Bab al-Mandab, wadda ke ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin safarar jiragen ruwa tsakanin Bahar Maliya da Tekun Indiya.
Bayan sanar da ƙwace Dhubab da Mayun, ƙungiyar Houthi ta ce mashigar Bab al-Mandab a buɗe take ga dukkan jiragen ruwa, sai dai waɗanda take zargin suna da alaƙa da Saudiyya.
Houthi ta bayyana matakin a matsayin martani ga takunkumin da Saudiyya ta kakaba wa yankunan da take iko da su, tana mai cewa matakin na daga cikin abin da ta kira "takunkumin ramuwar gayya" , da nufin karya abin da ta bayyana a matsayin katangar takunkumin da aka sanya mata.
Ƙaruwar ikon Houthi a wannan muhimmin yankin na iya ƙara tayar da hankalin ƙasashen duniya, musamman saboda Bab al-Mandab na daga cikin manyan hanyoyin da ake bi wajen safarar kayayyaki da makamashi a duniya.
