Hukumar Kare Farar Hula ta Saudiyya ta ce wasu benaye na ginin, wanda ke ɗauke da hedikwatar asusun babban birnin ƙasar, sun samu lahani sakamakon harin.
Sa'o'i kaɗan kafin tabbatar da ɓarnar, kakakin ƙawancen sojojin Saudiyya ya bayyana cewa tarkacen wani makami mai linzami da aka yi nasarar kakkaɓowa ne ya haddasa ɓarnar da aka gani a Riyadh.
Sai dai shaidun gani da ido sun ce sun ga alamun ɓarna a hasumiyar ginin.
A kwanakin baya-bayan nan, hare-haren mayaƙan Houthi na Yemen kan biranen Saudiyya sun ƙaru.
Mintuna kaɗan bayan bayyana labarin harin, Ma'aikatar Harkokin Wajen Qatar ta fitar da sanarwar Allah wadai da abin da ta kira "ci gaba da kai hare-hare" kan Masarautar Saudiyya, waɗanda suka haifar da ɓarna a babbar cibiyar kasuwanci ta Sarki Abdullah da ke Riyadh.
Haka kuma, Ma'aikatar Harkokin Wajen Kuwait ta bayyana harin a matsayin "keta hurumin ikon mallakar ƙasa na Masarautar Saudiyya a fili."
