Hukumar ta yi gargaɗin cewa kamfanonin da suka ƙi bin wannan umarni za su fuskanci hukunci bisa tanade-tanaden dokokin ƙasar.
Umarnin ya shafi kamfanonin musayar kuɗaɗen kirifto, tura kuɗi, adana kuɗi, cinikayya, biyan kuɗi, bayar da rance da sauran ayyukan kuɗi da ake gudanarwa ta hanyar intanet.
A cikin sanarwar da ta fitar, NRS ta ce bayan kammala rajistar kafin ranar 30 ga Nuwamba, ana buƙatar kamfanonin su haɗa tsarin gudanar da ayyukansu da sabon shafin rajistar haraji kafin ranar 31 ga Disamban 2026.
Hukumar ta bayyana cewa matakin ya yi daidai da tanade-tanaden dokokin haraji na shekarar 2025, waɗanda suka wajabta wa masu gudanar da irin waɗannan ayyuka yin rajista, adana bayanan hada-hadar kuɗaɗensu, gabatar da rahotanni da kuma biyan haraji.
NRS ta ce sabon tsarin zai taimaka wajen sa ido kan harkokin kuɗi, da kuma yaƙi da safarar kuɗaɗen haram, tallafa wa ta'addanci da kuma yaɗuwar makamai ba bisa ƙa'ida ba.
Ta ƙara da cewa wajabcin yin rajistar ya shafi dukkan kamfanonin da ke gudanar da harkokin kadarorin dijital a Nijeriya ko kuma waɗanda 'yan ƙasar ke amfani da ayyukansu, ko da kuwa suna da ofis a cikin ƙasar ko kuma ba su da shi.
