Gwamnatin Jihar Sokoto ta sanar da rufe Masallacin Juma’a na Musa Lukuwa har sai yadda hali ya yi, bayan wani tashin hankali da ya faru a makon da ya gabata, inda wani matashi ya daba wa limamin wuƙa.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na gwamnatin jihar, Abubakar Bawa , ya fitar, gwamnatin ta ce an ɗauki matakin ne domin bai wa hukumomi damar gudanar da cikakken bincike kan harin da kuma abubuwan da suka haddasa shi.

Gwamnatin ta kuma kafa wani kwamitin malamai domin bincikar musabbabin rikicin, tare da sa ran kwamitin zai gabatar da shawarwari kan matakan da ya dace a ɗauka domin hana sake faruwar irin wannan lamari.

Sanarwar ta ce gwamnatin jihar ta nesanta kanta daga duk wani yunƙuri na fakewa da addini wajen yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW) .

Gwamnatin ta kuma yi kira ga al’ummar jihar da su guji furta kalaman da za su iya tayar da hankali, tunzura jama’a ko kawo cikas ga zaman lafiya da haɗin kan al’umma.

Wanene Musa Ayuba Lukuwa?

Malam Musa Ayuba Lukuwa malamin addinin Musulunci ne a Jihar Sokoto, wanda ake danganta shi da fahimtar Ahlussunnah Wal Jama’a .

Malamin ya yi suna wajen bayyana ra’ayoyinsa kan wasu batutuwa masu sarkakiya da suka shafi fikihu da wasu ayyukan ibada.

Daga cikin batutuwan da ya taɓa yin bayani a kai akwai batun tabbatar da ganin jinjirin wata kafin bukukuwan Musulunci, inda ya jaddada muhimmancin dogaro da ganin wata a cikin gida ko yankunan da ke kusa.

A baya-bayan nan, hotuna da bidiyoyi da aka yaɗa a kafafen sada zumunta sun nuna malamin ɗauke da bindiga, bayan rahotannin fuskantar barazana da ake dangantawa da zargin taɓa mutuncin Annabi Muhammad (SAW).

Sai dai hukumomi na ci gaba da bincike kan abubuwan da suka faru da kuma musabbabin tashin hankalin da ya kai ga rufe masallacin.