An cimma wannan matsaya ne a ƙarshen taron sulhu tsakanin Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), wanda aka gudanar a Abuja ranar Talata.
Ma’aikatar Ƙwadago da Samar da Ayyukan Yi ce ta shirya taron domin tattauna batutuwan da suka shafi walwala da jin daɗin ma’aikata, bayan da NLC ta buƙaci inganta yanayin aiki tare da samar da tallafin da zai rage musu matsin tattalin arziƙi.
Tawagar Gwamnatin Tarayya, wadda ta haɗa da Ministan Ƙwadago, Dokta Muhammad Dingyadi, da Darakta Janar na Kasafin Kuɗi, Tanimu Yakubu, ta sanya hannu kan yarjejeniyar tare da Shugaban NLC, Joe Ajaero.
Ma’aikata Za Su Samu Tallafin na Watanni Shida
Bisa yarjejeniyar da aka cimma, za a biya alawus ɗin sufuri ga ma’aikata a matakan gwamnati daban-daban na tsawon watanni shida, daga Nuwamba 2026.
Ana sa ran wannan mataki zai taimaka wajen rage nauyin kuɗaɗen sufuri da ma’aikata ke fuskanta sakamakon tsadar rayuwa.
Za a Biya Ma’aikatan Lafiya Bashin Alawus
Taron ya kuma amince cewa za a biya ma’aikatan lafiya alawus-alawus na watanni 19 da ake bin su cikin watanni uku, daga watan Disamba 2026.
Haka kuma, ɓangarorin biyu sun amince da kafa kwamiti da zai fara aiki nan take domin tattauna batun mafi ƙarancin albashi na ƙasa.
A ƙarshen taron, wakilan gwamnati da na ƙwadago sun amince za su sake zama bayan wata guda domin duba yadda ake aiwatar da yarjejeniyar da kuma tantance ci gaban da aka samu kan batutuwan da suka tattauna.
