Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) ne ya ruwaito hakan a ranar Litinin.

A safiyar Litinin, jami'an tsaro sun kama wasu matasa 25 a wani gida da ke yankin arewacin babban birnin ƙasar, Bissau, kamar yadda wani jami'in rundunar tsaron ƙasar (National Guard) ya shaida wa AFP.

Jami'in ya ce rukunin mutanen ya ƙunshi 'yan ƙasar Mali 10, Senegal 10, Guinea uku da kuma Guinea-Bissau biyu.

Ya bayyana cewa an shirya jigilar mutanen zuwa wani tsibiri da ke cikin tarin tsibiran Bijagos, wanda aka tanada a matsayin wurin haɗuwa kafin tafiyarsu zuwa Tsibiran Canary.

A ranar Asabar ma, jami'an tsaro sun kama wasu mutane da ke ƙoƙarin yin hijira a tashar jiragen ruwan kamun kifi ta Bandim da ke birnin Bissau.

Wani jami'in National Guard ya ce an kama wani tsohon jirgin ruwa na katako mai suna Pirogue, wanda ke ɗauke da mutane 143.

A cewar jami'in, matsin lambar da ake yi kan hanyoyin safarar mutane ba bisa ƙa'ida ba a Senegal na ƙara tilasta wa masu shirya irin waɗannan tafiye-tafiye neman wasu wuraren tashi da ba a cika sanya musu ido ba, musamman a ƙasashen Gambia da Guinea-Bissau.

A cikin 'yan watannin nan, an ceto daruruwan mutane, mafi yawansu daga Senegal, Gambia, Guinea da Mali, a gabar tekun yammacin Afirka bayan samun kansu cikin haɗarin jiragen ruwa.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, dubban mutane sun mutu ko kuma suka ɓace a cikin teku yayin ƙoƙarin isa Turai ta waɗannan hanyoyi masu haɗari.