A cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na sada zumunta ranar Talata, EFCC ta ce jami’anta na ofishin shiyya ta biyu da ke Legas ne suka gano wurin a ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026.
Hukumar ta bayyana cewa samamen ya biyo bayan tattara bayanan sirri da kuma sa ido kan ayyukan mutanen da ake zargin suna sarrafa mai ba bisa ƙa’ida ba.
A cewar sanarwar, babu kowa a wurin lokacin da jami’an suka isa. Sai dai sun gano ragowar kayayyakin da ake zargin an yi amfani da su wajen tace mai, da kuma wasu tankuna da aka binne a ƙarƙashin ƙasa domin narkawa da sarrafa man.
EFCC ta ce biyu daga cikin tankunan da aka gano suna ɗauke da wasu abubuwa da ake zargin man dizal ne.
Binciken farko ya kuma nuna cewa waɗanda ake zargin suna haƙo ɗanyen mai daga Warri a Jihar Delta da kuma Fatakwal a Jihar Ribas, sannan su kai shi matatar da ke Ogere domin sarrafawa.
Hukumar ta ce ana zargin masu gudanar da wurin da amfani da zafi mai tsanani wajen tace sinadaran ɗanyen man domin samar da dizal da za a sayar a kasuwar Nijeriya.
Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an tsaro da ke wurin sun shaida wa EFCC cewa waɗanda ake zargin ’yan China ne, sai dai ba a bayyana sunayensu ko sunan kamfanin da ake zargin yana da alaƙa da matatar ba.
Hukumar ta ce jami’anta sun karɓe iko da wurin, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano mutanen da ke da hannu a lamarin, tabbatar da masu mallakar wurin da kuma tantance girman ayyukan da ake zargin haramtattu ne.
EFCC ta ƙara da cewa samamen ya biyo bayan wani aikin da ta gudanar a baya, inda ta rufe wasu masana’antun sarrafa lithium guda huɗu da ake zargin suna aiki ba bisa ƙa’ida ba a yankin.
