Jimillar bashin da ake bin Nijeriya a ƙasashen waje ya kai dala biliyan 145.02 a ƙarshen shekarar 2025, daga dala biliyan 135.99 a shekarar 2024, wanda ke nuna ƙarin kusan kashi 6.6 cikin 100.

Rahoton ƙididdigar basussukan ƙasashen duniya na Bankin Duniya na shekarar 2026 ya nuna cewa wannan ƙarin bashin na daga cikin matsalolin da ke ƙara jefa ƙasashe masu tasowa cikin matsin lambar kuɗi.

Rahoton ya bayyana cewa adadin bashin ya ƙunshi basussukan da ke kan gwamnati da kuma na kamfanoni masu zaman kansu, don haka ya bambanta da jimillar bashin da gwamnatin Nijeriya kaɗai take bi.

Bankin Duniya ya kuma bayyana cewa bashin ƙasashe masu tasowa ya ƙaru da kashi 5.5 cikin 100, inda ya kai dala tiriliyan 9.4 a shekarar 2025.

A cewar bankin, wannan shi ne ƙarin da ya fi sauri a kowace shekara tun daga 2021, yayin da gwamnatoci suka koma kasuwannin lamuni na ƙasashen duniya, tare da ƙara dogaro da masu ba da lamuni masu zaman kansu, waɗanda galibi ke bayar da rance da ruwa mai yawa.

Bankin Duniya ya yi gargaɗin cewa hauhawar basussuka da kuɗaɗen da ake kashewa wajen biyan su na iya rage kuɗaɗen da gwamnatoci ke da su na gudanar da muhimman ayyuka, ciki har da kiwon lafiya, ilimi, samar da ababen more rayuwa da ayyukan yi.

Haka kuma, bankin ya lura cewa wasu gwamnatoci na fitar da sabbin takardun lamuni domin biyan tsofaffin basussukan da wa'adin biya ya yi, lamarin da kan tsawaita lokacin biyan bashin, amma wani lokaci ya sa su karɓi sabon lamuni mai tsadar ruwa ba tare da rage nauyin bashin da ke kansu ba.

A Nijeriya kuwa, bayanai daga Ofishin Kula da Basussuka (DMO) sun nuna cewa Bankin Duniya ne babban mai ba da lamuni na ƙasashen waje ga ƙasar a ƙarshen watan Yunin 2026, inda yake bin Nijeriya dala biliyan 20.73.

Haka kuma, bashin da aka samu ta hanyar sayar da takardun Eurobonds ya kai dala biliyan 18.55, wanda ke wakiltar wani babban kaso na bashin waje na ƙasar.

Alƙaluman DMO sun nuna cewa Nijeriya ta kashe dala biliyan 1.82 wajen biyan bashin ƙasashen waje a cikin watanni shida na farkon shekarar 2026.

Daga cikin wannan kuɗi, an kashe dala biliyan 1.11 wajen biyan kuɗin ruwa, wanda ya kai kusan kashi 61 cikin 100 na jimillar kuɗin da aka biya a wannan lokacin.

Binciken Bankin Duniya ya nuna irin ƙalubalen da ƙasashe masu tasowa ke fuskanta wajen daidaita biyan basussuka da kuma buƙatar samar da kuɗaɗen gudanar da ayyukan gwamnati da muhimman shirye-shiryen ci gaba.