Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sanar da cewa za ta ƙaddamar da gangamin yaƙin neman sake zaɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a jihar Kaduna ranar 24 ga Oktoban 2026.

A cikin wata sanarwa da Darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar, Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar, ya fitar, APC ta ce taron na Kaduna zai zama farkon zagayen gangamin neman goyon baya a faɗin jihohi 36 na Najeriya da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta ɗauki wasu matakai masu wahala na gyaran tattalin arziki, waɗanda a cewar jam’iyyar, gwamnatocin baya suka ƙaurace wa ɗauka.

Saboda haka, APC ta yi kira ga ’yan Najeriya da su sake zaɓar Tinubu domin ya samu ƙarin wa’adi na shekaru huɗu don kammala sauye-sauyen da gwamnatinsa ta fara.

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga mambobinta, shugabanninta da magoya bayanta da su fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu domin halartar taron da za a gudanar a Kaduna.

Ta jaddada cewa samun nasara a babban zaɓen shekarar 2027 ya danganta da ƙarfafa ayyukan jam’iyyar tun daga matakin gundumomi har zuwa rumfunan zaɓe.

Sanarwar ta ƙare da kira ga shugabanni da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da su fara shirye-shiryen wayar da kan masu zaɓe, tare da tabbatar da cewa dukkan ayyukan gangamin za su gudana cikin lumana.