Rahotanni sun ce haɗarin ya faru ne a yankin Ukubie da ke Ƙaramar Hukumar Kudancin Ijaw, lokacin da jirgin ke ɗauke da mutane da dama.
Bayanai sun nuna cewa jirgin ya cika maƙil da fasinjoji a lokacin da ya kife, lamarin da ya janyo fargabar mutuwar mutane da dama tare da ɓacewar wasu a cikin ruwa.
Tsohon shugaban ma'aikatan sufurin jiragen ruwa, Ipigansi Ogoniba, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust aukuwar lamarin, sai dai ya ce bai iya tantance ainihin adadin mutanen da abin ya shafa ba.
Shi ma kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Musa Muhammad, ya tabbatar da aukuwar haɗarin.
Jihar Bayelsa na daga cikin jihohin Nijeriya da ake amfani da jiragen ruwa wajen sufuri, musamman a yankunan da ruwa ya mamaye. Sai dai a lokuta da dama ana samun haɗurran jiragen ruwa sakamakon cunkoson fasinjoji da kuma rashin amfani da rigunan kariya daga nutsewa a ruwa.
