top stories
An Yi Jana’izar Mijin Shugabar Tanzania
An yi jana’izar Hafidh Ameir Hassan, mijin Shugabar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, a Kizimkazi da ke Zanzibar. Marigayin, wanda aka haifa a ranar 1 ga Janairu, 1946, ya rasu ne a ranar Litinin, 7 ga Satumba, bayan fama da matsalar zuciya. Mataimakin Shugaban Tanzania, Deogratius Ndejembi, ne ya sanar da rasuwar, inda ya ce Hafidh Ameir Hassan ya rasu da misalin ƙarfe 8:00 na safe agogon ƙasar. Ya rasu ne a Asibitin Emilio Mzena Memorial da ke Zanzibar, inda yake karɓar magani. Jana’izar marigayin ta gudana a garinsu na Kizimkazi, inda iyalai, ’yan uwa da sauran al’umma suka halarta domin yi ma
azubairu (legacy byline) · 8 Sat, 2026, 13:26
An yi jana’izar Hafidh Ameir Hassan, mijin Shugabar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, a Kizimkazi da ke Zanzibar.
Marigayin, wanda aka haifa a ranar 1 ga Janairu, 1946, ya rasu ne a ranar Litinin, 7 ga Satumba, bayan fama da matsalar zuciya.
Mataimakin Shugaban Tanzania, Deogratius Ndejembi, ne ya sanar da rasuwar, inda ya ce Hafidh Ameir Hassan ya rasu da misalin ƙarfe 8:00 na safe agogon ƙasar.
Ya rasu ne a Asibitin Emilio Mzena Memorial da ke Zanzibar, inda yake karɓar magani.
Jana’izar marigayin ta gudana a garinsu na Kizimkazi, inda iyalai, ’yan uwa da sauran al’umma suka halarta domin yi masa bankwana.