Jami'an tsaro a jihar California ta Amurka sun kama wani mutum ɗauke da bindiga a filin wasan golf mallakin Shugaban Amurka, Donald Trump, gabanin ziyararsa domin halartar wani taron tara kuɗaɗe na Jam'iyyar Republican.
Masu bincike sun bayyana cewa mutumin, mai suna Jeanine John Tael , mai shekaru 38, an kama shi ne a filin wasan golf da ke Rancho Palos Verdes , tare da bindiga da kuma wasu alburusai da ake zargin haramtattu ne.
A cewar 'yan sanda, an ga mutumin yana yawo a sassa daban-daban na filin wasan, yana ɗaukar hotuna da bidiyo tare da lura da shirye-shiryen tsaro da ake yi kafin isowar Shugaba Trump.
Rahotanni sun ce an kama shi ne ranar Lahadi, kuma a halin yanzu yana tsare a hannun jami'an tsaro yayin da yake fuskantar zarge-zargen ɗauke da bindiga a ɓoye ba tare da izini ba da kuma mallakar haramtattun alburusai.
Jami'an tsaro sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano dalilin kasancewar mutumin a wurin da kuma ko akwai wata barazana da ya ke shirin haifarwa.
