Masana binciken tarihi sun gano wani ɓurɓushin kwanson dodon koɗi da ake kyautata zaton ya kai shekaru 66,000 , a wani wurin binciken kayan tarihi da ke Ankara, babban birnin Turkiyya.

Ministan Al’adu da Yawon Buɗe Ido na Turkiyya, Mehmet Nuri Ersoy , ne ya bayyana gano ɓurɓushin, yana mai cewa an same shi ne yayin aikin haƙar kayan tarihi a Kulhöyük , da ke unguwar Oyaca a gundumar Gölbaşı ta Ankara.

Ersoy ya ce an gano kwanson ne a wani yanki da ake ganin ya taɓa kasancewa kusa da Tekun Tethys , wani tsohon babban teku da ya taɓa mamaye wasu sassan yankin da a yau ake kira tsakiyar Anatoliya.

Ya bayyana hakan a shafukan sada zumunta ranar Litinin, inda ya ce binciken na iya samar da muhimman bayanai kan tarihin yankin.

Yadda kwanson ya isa wurin

Masu bincike yanzu na nazarin ko mutanen da suka zauna a Kulhöyük ne suka gano kwanson a wani wuri daban sannan suka kawo shi wurin zamansu da gangan.

Idan binciken ya tabbatar da hakan, masana sun ce hakan na iya taimakawa wajen fahimtar yadda aka samo kwanson da kuma irin muhimmancin da mutanen zamanin suka iya ba shi.

Kulhoyuk: tsohon wurin zama

Kulhöyük wani tsohon wurin zama ne da aka kiyasta yana da kusan shekaru 5,000 , kuma ana danganta shi da tsoffin wayewar kan al’ummomin Hattian da Hittite .

Saboda haka, halittar da ta samar da wannan ɓurɓushin kwanson ta rayu dubban shekaru kafin mutanen da suka zauna a Kulhöyük.

An fara aikin haƙa kayan tarihi a wurin tun shekarar 2021 , a ƙarƙashin wani shirin bincike na dogon lokaci da fadar shugaban ƙasar Turkiyya ke tallafawa.

Mataimakiyar Farfesa Derya Yılmaz Tekin ce ke jagorantar aikin a madadin Jami’ar Ankara da Ma’aikatar Al’adu da Yawon Buɗe Ido.

Ministan ya ce za a ci gaba da aikin binciken domin ƙara fahimtar tarihin Kulhöyük da gano wasu sabbin abubuwa da ka iya ƙara haske kan yadda mutane suka rayu a yankin tun zamanin da.