Samamen ya gudana ne a ƙauyen Kiniso, kusa da Ajue, da ke Ƙaramar Hukumar Odigbo ta jihar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Abayomi Jimoh, ne ya tabbatar da kamen cikin wata sanarwa da ya fitar a Akure ranar Talata.

Jimoh ya ce an fara binciken ne bayan wani mutum mai suna Yusuf Nasiru ya kai ƙara cewa wasu mutane biyu, Peter Desmond da Olami Toro, sun je shagonsa da ke Okitipupa a ranar 25 ga Oktoba, domin neman sauya dalar Amurka zuwa Naira.

A cewarsa, Nasiru ya miƙa musu dala 6,000, wadda ta kai kimanin naira miliyan 8 da dubu 600.

Sai dai, maimakon su ba shi kuɗin Naira, waɗanda ake zargin sun mayar masa da dalolin, suna masu cewa ba su da isassun kuɗaɗen da za su kammala cinikin, kafin su bar wurin.

Daga baya, Nasiru ya gano cewa dalolin jabun kuɗi ne, lamarin da ya sa ya kai ƙara ga ’yan sanda a ranar 28 ga Oktoba.

Jimoh ya bayyana cewa jami’an rundunar ’yan sandan reshen Okitipupa sun fara bincike, inda suka yi amfani da bayanan sirri da hanyoyin bin diddigin fasaha wajen gano inda Desmond yake a ƙauyen Kiniso.

A ranar 29 ga Oktoba, jami’an ’yan sandan suka kai samame wurin da ake zargin ana amfani da shi wajen ƙera da buga jabun daloli domin damfarar jama’a.

A yayin samamen, an kama Desmond, yayin da sauran mutanen da ke wurin suka tsere ta katangar harabar ginin.

Haka kuma, jami’an sun ƙwato buhuna uku ɗauke da takardun dalar Amurka da ake zargin na jabu ne, tare da wani ƙaramin akwati na katako.

Kakakin rundunar ya ce wanda aka kama yana taimaka wa jami’an tsaro da bayanai masu amfani, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.