Ambaliya ta lalata gidaje da gonaki bayan Dam ɗin Jan Gefe da ke Karamar Hukumar Ghari a Jihar Kano ya balle.

Mataimakiyar Shugabar Karamar Hukumar Ghari, Hon. Aisha Lawan ’Yan Dadi, ce ta bayyana hakan.

Aisha ta ce, dam ɗin ya balle ranar Juma’ar data gabata inda ambaliyar ta lalata gidaje da gonaki tare da tafiya da dabbobi.

Ta ce, lamarin ya tilasta wa wasu mazauna yankin hijira zuwa Katsina da wasu yankunan Zariya.

Aisha ta ƙara da cewa ƙauyuka 61 a mazabun ’Yan Dadi, Shuwaki da Bumai ne ke amfani da dam ɗin wajen samun ruwan sha, bukatun yau da kullum da noman rani.

Ta ƙara da cewa, bayan sa’o’i 24 da faruwar lamarin ta sanar da Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, wanda ya tura tawagar da ta haɗa da Kwamishinan Ayyuka, Shugaban Hukumar SEMA, wakilan NEMA, da Mai Bai wa Gwamnan Shawara kan Ayyukan Jin Kai domin duba halin da ake ciki da ɗaukar matakin gaggawa.

Aisha ta ce, tawagar ta tabbatar wa al’ummar yankin cewa za a fara aiki kan matsalar a yau Litinin tare da kammala wa cikin ƙanƙanin lokaci.