Maharan sun kai hari ƙauyen Binnari, da ke Ƙaramar Hukumar Karim Lamido, jim kaɗan bayan sallar Juma’a, inda suka riƙa harbin mutane ba tare da nuna bambanci ba. Sun kuma sace kayan abinci tare da ƙona shaguna da babura.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, Victor Mshelizah, ya shaida wa BBC cewa adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru ne bayan gano ƙarin gawawwaki 23 a ranar Lahadi.
A cewarsa, binciken ’yan sanda ya nuna cewa wasu daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su sun nutse a ruwa ne yayin da suke ƙoƙarin tserewa daga maharan, yayin da aka kashe wasu a dazukan da ke kusa da ƙauyen.
Wasu mazauna yankin sun ce maharan sun shigo ƙauyen ne daga Jihar Filato da ke makwabtaka da Taraba, ɗauke da muggan makamai.
A nata ɓangaren, ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta zargi hukumomi da gazawa wajen kare mazauna ƙauyuka daga hare-haren ’yan bindiga.
Ya zuwa yanzu, babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.
Jihar Taraba da wasu sassan Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro da suka haɗa da hare-haren ’yan bindiga da sace mutane domin karɓar kuɗin fansa.
