Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Najeriya (ACF) ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta rage mayar da hankali kan shirye-shiryen zaɓen 2027, tare da karkata hankalinta wajen magance matsalar rashin tsaro da ke addabar ƙasar.
Ƙungiyar ta bayyana cewa ci gaba da kai hare-hare, kashe-kashe, garkuwa da mutane da lalata hanyoyin samun abin dogaro da kai da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke yi, na barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin Najeriya.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran ƙungiyar, Farfesa Tukur Muhammad Baba, ya fitar, ACF ta nuna damuwarta kan abin da ta bayyana a matsayin rashin mayar da hankali yadda ya kamata wajen magance matsalar tsaro da ɗaukar matakan da suka dace kan masu aikata laifuka.
Ƙungiyar ta ce lokaci ya yi da za a dakatar da rikicin siyasa tare da mayar da hankali wajen kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro.
ACF ta kuma nuna damuwarta kan ci gaba da garkuwa da mutane, musamman ɗaliban da ake zargin suna hannun masu garkuwa da su a jihohin Borno da Kwara da wasu sassan ƙasar.
Sanarwar ta ƙara da cewa hare-hare, kashe-kashe da garkuwa da mutane na ci gaba da faruwa a jihohin Zamfara, Filato, Taraba, Benue, Neja, Katsina, Kaduna da Kogi.
Ƙungiyar ta buƙaci gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da dawo da zaman lafiya a yankunan da matsalar tsaro ta shafa.
A cewar ACF, tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya na daga cikin manyan nauyin da ke kan gwamnati, don haka bai kamata shirye-shiryen siyasa da zaɓe su rinjayi ƙoƙarin magance matsalar tsaro ba.
