AMMASCO RADIO NEWSROOM

Na gida

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Naira Tiriliyan 11 A Matsayin Burin Kuɗaɗen Shiga Na Hukumar Kwastam A 2026

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da buƙatar Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) na tara sama da Naira tiriliyan 11 a matsayin kuɗaɗen shiga na shekarar 2026. A yayin nazarin rahoton Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Kwastam da Harajin Kaya, 'yan majalisar sun yaba da irin nasarorin da hukumar ta samu a shekarar kasafin kuɗi ta 2025. Majalisar ta lura cewa Hukumar Kwastam ta zarce burin tara kuɗaɗen shiga da aka sa mata a shekarar 2025, inda ta tara Naira tiriliyan 7.2 maimakon Naira tiriliyan 6.5 da aka tsara, wanda ya nuna ƙarin sama da kashi 10 cikin ɗari. Domin cimma sabon buri na

EFCC Ta Miƙa Kayan Da Aka Kwato Daga Masu Laifi Ga Ma'aikatar Ilimi

Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta miƙa wasu kayayyakin da aka ƙwato daga hannun masu aikata laifuka ga Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, domin amfanin ɓangaren ilimi. Kayayyakin sun haɗa da gadajen bene masu hawa biyu guda 501, katifu guda 939 da kuma gadaje na katako guda 12, waɗanda aka ƙwato yayin wani samame na musamman da EFCC ta gudanar kan masu aikata laifukan yanar gizo. Hukumar ta bayyana cewa an danganta kayayyakin da mutane 792 da ake zargi da aikata laifuka, ciki har da baƙi 193 daga ƙasashen waje, waɗanda aka gurfanar a kotu kafin daga bisani a maya

Yan Sanda A Kaduna Sun Kama Mutane Shida Kan Kisan Matafiya Biyu Ta Hanyar Taron Dangi

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna ta yi Allah wadai da kisan wasu matafiya biyu, Muhammadu Sani da abokinsa Aliyu Mohammed, dukkansu mazauna ƙauyen Umar da ke ƙaramar hukumar Igabi, waɗanda wasu fusatattun mutane suka kashe bisa zargin sata. A wata sanarwa da Jami'in Hulɗa da Jama'a na Rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce marigayin da abokinsa na kan hanyarsu ta zuwa Tudun Wada da ke Zariya ne domin duba wani baffansu da ke kwance jinya, inda suke tafiya da sabuwar babur. Sanarwar ta ce wasu mutane sun yi musu kuskuren zargin cewa ɓarayi ne, kuma duk da ƙoƙarin da suka yi na bayyana ka

Tinubu Ya Karɓi Baƙuncin Ƙaramin Ministan Harkokin Wajen Daular Larabawa

Alamu na nuna cewa Najeriya da Daular Larabawa (UAE) na ƙara ƙarfafa alaƙar diflomasiyya da tattalin arzikinsu, yayin da ƙasashen biyu ke kammala shirye-shiryen kafa Kwamitin Haɗin Gwiwa na Dindindin domin bunƙasa haɗin gwiwarsu. A wannan ƙoƙari ne Ƙaramin Ministan Harkokin Wajen Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Shakhboot Bin Al Nahyan, ya kai ziyarar aiki ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Talata. Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ce ta raka baƙon ministan zuwa ganawar da shugaban ƙasar. Da take jawabi bayan ganawar, Bianca

Kotun Majistare Ta Yanke Wa Direba Hukuncin Aikin Al'umma Da Tara Saboda Tukin Ganganci

Kotun Majistare da ke Wuse a Abuja ta yanke wa wani direba mai suna Atada Victor hukuncin yin aikin al'umma na tsawon makonni biyu, tare da biyan tarar kuɗi da diyya da suka kai Naira miliyan 1.08, bayan samunsa da laifin tukin ganganci, cin zarafin jami'in Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) da kuma sauran laifukan karya dokokin hanya. A cikin wata sanarwa da Jami'in Yaɗa Labarai na FRSC, Osondu Ohaeri, ya sanya wa hannu, ya ce lamarin ya faru ne yayin da jami'an hukumar ke gudanar da sintiri na yau da kullum a Babban Birnin Tarayya, Abuja. Sanarwar ta ce jami'an FRSC sun yi ƙoƙarin tsayar

Ma'aikatar Tsaro Ta Bukaci Kamfanonin Tsaro Masu Zaman Kansu Su Yi Amfani Da Fasahar Tattara Bayanai

Ma'aikatar Tsaro ta Tarayya ta buƙaci kamfanonin tsaro masu zaman kansu a Najeriya su rungumi amfani da fasahar zamani da tsarin tattara bayanan sirri domin ƙarfafa gudummawar da suke bayarwa wajen inganta tsaron ƙasa. An bayyana wannan kira ne a yayin wani taron yini guda kan harkokin tsaro da aka gudanar a Abuja, inda masana tsaro, masu tsara manufofi da masu ruwa da tsaki suka tattauna hanyoyin sauya tsarin ayyukan kamfanonin tsaro daga dogaro da yawan jami'ai zuwa tsarin da ke amfani da bayanan sirri da fasahar zamani. A cikin saƙon da ya aike wa taron, Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Mohamm

Gwamna Zulum Ya Ƙaddamar Da Noman Damina Na 2026 Da Rarraba Kayan Tallafin Noma A Borno

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ƙaddamar da shirin noman damina na shekarar 2026, tare da fara sayar da takin zamani a farashin da gwamnati ta amince da shi, da kuma raba kayan tallafin noma kyauta ga manoma a faɗin jihar. Tallafin ya shafi ƙananan manoma, masu rauni, matasa, mata da kuma manoman da suka koma garuruwansu bayan sun rasa matsugunansu sakamakon matsalolin tsaro. Gwamnatin jihar ta bayyana cewa shirin na da nufin bunƙasa harkar noma, ƙarfafa samar da abinci, inganta tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa zaman lafiya da ci gaban al'ummomi. Haka

Gwamnatin jihar Kano ta gudanar da bikin yaye rukunin farko tare da kaddamar da sabon rukuni na matasa karkashin shirin bunkusa shugabanci da kwarewa a fannin lafiya

Bikin ya kunshi karrama waɗanda suka kammala shirin, tare da ƙaddamar da sabon rukuni na waɗanda za su shiga domin ci gaba da koyo hanyoyin inganta ayyukan kiwon lafiya a Najeriya. Dayake Jawabi Gwamnan Kano Alhaji Abba kabir yusuf, Wanda kwamishinan Lafiya na Jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya wakilta, ya bayyana shirin a matsayin muhimmin yunkuri da zai taka rawa wajen samar da ƙwararrun matasa a fannin lafiya da za su taimaka wajen inganta tsarin kiwon lafiya da kuma tabbatar da ci gaban harkokin kiwon lafiya a Jihar Kano da Najeriya Daga karshe gwamnan yayi kira ga sabbin matasan da suka

Gwamnatin Najeriya ta bukaci dillalan man fetur dasu gaggauta rage farashin mai sakomakon faduwar farashin danyen man a duniya

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buƙaci masu hada-hadar man fetur a faɗin ƙasar su gaggauta rage farashin litar fetur da sauran kayayyakin mai, biyo bayan faduwar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya. Gwamnatin ta bayyana cewa saukar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya kamata ya bayyana a farashin da ake sayar da fetur da sauran kayayyakin mai a cikin gida. A cewar gwamnatin, babu wani dalili da zai sa a ci gaba da sayar da fetur da tsohon farashi, alhali farashin ɗanyen mai ya ragu a kasuwannin duniya. Ta jaddada cewa rage farashin zai taimaka wajen sauƙaƙa wa ’yan Najeriya matsin tattal

Sama da Mutane 10,000 Sun Nemi Guraben Aikin Koyarwa 1,000 a Nasarawa

Sama da mutum 10,000 ne suka nemi guraben aikin koyarwa 1,000 a makarantun firamare da Gwamnatin Jihar Nasarawa ta amince da ɗauka ƙarƙashin wani shiri na musamman da aka tanada domin inganta ilimi a yankunan karkara. Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Nasarawa kan Harkokin Jama’a, Peter Ahemba , ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na wata biyu-biyu da aka gudanar a Sakatariyar Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Nijeriya (NUJ) reshen jihar da ke Lafiya. A cewarsa, ɗaukar malaman ya biyo bayan amincewar gwamnatin jihar da shirin samar da malamai 1,000 domin cike giɓin ƙarancin malamai

Gwamnatin Tinubu ta ciyo bashin Dala biliyan 11.4 daga bankin duniya cikin shekara uku

Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta samu rancen da ya kai Dala biliyan 11.4 daga Bankin Duniya tsakanin watan Yunin 2023 zuwa Yunin 2026, kamar yadda wani sabon bincike ya bayyana. Binciken ya nuna cewa wannan adadi ya kai kusan kashi 78 cikin 100 na Dala biliyan 14.59 da gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta samu daga Bankin Duniya cikin shekaru takwas da ta yi kan mulki. Rahoton ya kuma bayyana cewa idan aka amince da ƙarin rancen Dala biliyan 3.19 da gwamnatin Tinubu ta nema, jimillar bashin da za ta samu daga Bankin Duniyar za ta zarce wanda aka amince wa gwamnatin Buhari. Sai da

Dalilin dayasa hukumar zabe INEC ta sanar da tsawaita wa’adin rijistar masu zaɓe

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana dalilin da ya sa ta tsawaita wa’adin ci gaba da yin rajistar masu zaɓe (CVR) da ƙarin mako biyu a faɗin Najeriya. Mai magana da yawun hukumar, Zainab Aminu Abubakar, ta ce an ɗauki matakin ne domin bai wa ƴan Najeriya da suka cancanci yin rajista amma ba su samu damar yin hakan ba ƙarin lokaci, musamman matasan da suka cika shekara 18. A wata tattaunawa da ta yi da BBC, Aminu Abubakar ta bayyana cewa an fara aikin rijistar ne a matakai daban-daban tun daga watan Agustan shekarar 2025. Ta ce tun farko hukumar ta tsara kammala aikin rijistar

Gwamnatin shugaba Tinubu ta musanta sakaye Naira Triliyan 8 a kasafin kuɗin bara don zaben 2027

Gwamnatin shugaba Tinubu ta musanta sakaye kudi kimanin Naira Triliyan 8 a kasafin kuɗin bara don amfani da ita a zaɓe mai zuwa. Wannan na matsayin martani kan zargin da Atiku Abubakar Jagoran adawar ƙasar ya yi na cewa akwai wasu kuɗi da yawansu ya kai naira Triliyan 8 da wata Biliyan 8 ta daban da ba’a sanya su cikin kasafin kuɗi ba, kuma babu cikakken bayani kan abinda aka yi da su, a don haka ne yayi zargin cewa an zubasu cikin wata taskar adana kuɗaɗen yaƙin neman zaɓen baɗi. Ko da yake Atiku Abubakar yayi wannan zargi ne bisa dogaro ga rahoton asusun bayar da lamuni na IMF wanda ya fara

Za mu ɗaukaka ƙara kan hukuncin hana saka hijabi a makarantar Ibadan - MURIC

Ƙungiyar kare haƙƙoƙin Musulmi ta MURIC ta bayyana cewa ba ta amince da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta soke hukuncin da ya bai wa ɗalibai mata Musulmi damar sanya hijabi a makarantar International School, Jami'ar Ibadan (ISI) . A cikin wata sanarwa, MURIC ta ce za ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Koli, tana mai cewa hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar ya ƙunshi kura-kurai na shari'a. Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa ta riga ta shigar da takardar ɗaukaka ƙara tare da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin har sai Kotun Koli ta yanke hukunci na ƙarshe. Wannan mataki ya biyo bayan hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙa

INEC ta ƙara wa'adin rajistar masu zaɓe da mako biyu

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta sanar da ƙara wa'adin ci gaba da rajistar masu zaɓe na tsawon makonni biyu domin bai wa ƙarin ƴan Najeriya da suka cancanta damar yin rajista kafin babban zaɓen 2027. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Hukumar, Mohammed Kudu Haruna, ya sanya wa hannu, INEC ta ce ta ɗauki matakin ne bayan nazarin yadda aikin rajistar ke gudana da kuma la'akari da shawarwarin da ta samu daga ofisoshinta na jihohi, jam'iyyun siyasa, ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki. Hukumar ta bayyana cewa aikin rajistar, wanda ya fara a ranar 18 ga Agustan 202

Me ya sa wasu ƴan Kannywood ke fita daga ƙungiyar Triple R mai tallata Tinubu?

Wasu fitattun jaruman Kannywood na ci gaba da sanar da ficewarsu daga ƙungiyar Triple R Kannywood for Renewed Hope , wadda aka kafa domin tallata manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Na baya-bayan nan da ya sanar da ficewarsa shi ne fitaccen jarumi Rabiu Rikadawa , wanda ya ce ya ɗauki matakin ne saboda abin da ya bayyana a matsayin rashin tabbas da kuma rashin bin dokoki da ƙa'idojin ƙungiyar . A cewar Rikadawa, yadda ake tafiyar da harkokin ƙungiyar bai dace da abin da aka kafa ta a kai ba, lamarin da ya sa ya yanke shawarar ficewa. Kafin s

'Har yanzu muna ƙalubalantar shugabancin David Mark a ADC' — Nafi'u Bala

Ɗaya daga cikin ɓangarorin da ke rikici kan shugabancin jam'iyyar ADC, ƙarƙashin Nafi'u Bala Gombe, ya ce har yanzu suna ci gaba da ƙalubalantar shugabancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, duk da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke. Da yake zantawa da BBC Hausa, Nafi'u Bala ya ce har yanzu suna da ƙara a gaban kotu da ke ƙalubalantar sahihancin shugabancin David Mark, yana mai cewa mutanen da ke jagorantar jam'iyyar a yanzu ba halastattun mambobi ba ne. "Mu ne halastattun shugabannin jam'iyyar, kuma muna da ƙara da ke ƙalubalantar wannan shugabanci, da kuma sah

Kano Pillars ta naɗa Daniel Ogunmodede a matsayin sabon kocinta

Hukumar gudanarwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sanar da naɗin Daniel Ogunmodede a matsayin sabon babban kocin ƙungiyar domin jagorantar ta a kakar wasan firimiyar Najeriya ta 2026/2027. A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran ƙungiyar ya fitar a ranar Juma'a, an bayyana cewa Ogunmodede, wanda aka fi sani da "Ijaball", zai jagoranci harkokin fasaha na ƙungiyar yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen tunkarar sabuwar kakar wasa. Sanarwar ta ce naɗin nasa wani ɓangare ne na shirin sake fasalin ƙungiyar domin inganta bajintarta a gasannin cikin gida da kuma na nahiyar Afirka. Ogu

DSS Ta Gurfanar da Mutum Biyar Kan Zargin ɓoye Inda Timipre Sylva Yake

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Najeriya (DSS) ta gurfanar da wasu mutum biyar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zarginsu da ɓoye bayanai kan inda tsohon gwamnan Jihar Bayelsa kuma tsohon ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva , yake. A cewar DSS, ana zargin waɗanda ake tuhuma da haɗa baki wajen ɓoye inda Mista Sylva yake, wanda hukumar ta ce mutum ne da hukumomin tsaro ke nema. Dukkan waɗanda ake tuhuma sun musanta zarge-zargen da aka karanta musu a gaban kotu. Lauyan DSS, Emmanuel Orubor , ya roƙi kotun ta sanya ranar fara sauraron shari'ar domin gabatar da shaidu. A

Kotu Ta Fara Sauraron Ƙarar da Ke Kalubalantar Takarar Pantami a Gombe

Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta fara sauraron ƙarar da Khamisu Ahmed Mailantarki ya shigar, inda yake ƙalubalantar sahihancin takarar Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin ɗan takarar gwamnan jam'iyyar PDP . Mai ƙarar ya yi zargin cewa ba a bi ƙa'idojin jam'iyyar wajen zaɓen ɗan takarar ba, tare da neman kotu ta soke takarar Pantami. Sai dai waɗannan zarge-zarge na gaban kotu, kuma ba a yanke hukunci a kansu ba. A zaman kotun, lauyan INEC ya nemi ƙarin lokaci domin shigar da martanin hukumar, buƙatar da kotun ta amince da ita. Mai shari'a ta ɗage ci gaba da sauraron shari'ar zuwa 9 ga Yulin 2